Kungiyoyi ƙwadago na NLC da TUC sun sanar da janye yajin aikin da suka yi niyyar faraea daga gobe.
Wannan na zuwa ne bayan wata tattaunawa ta gaggawa da kungiyoyin suna yi da ɓangaren gwamnatin tarayya a yau.
Da ma dai a baya kungiyoyin ƙwadagon sun lashi takobin tafiya yajin aikin ne domin nuna nuna rashin amincewa da batun cire tallafin man fetur da gaza cika cika musu buƙatu bakwai da suka gundaya wa gwamnatin.
Janye yajin aikin har’ila yau, wani yunƙuri ne na ba wa gwamnati damar cika alƙawuran da ta yi a yayin wannan zama.
Don haka, mataimakin shugaban ƙungiyar ƙwadago, kwamared Adeyanju, ya umarci dukkan ma’aikata da su koma bakin aiki daga gobe.