‘Yar sama jannatin ƙasar Saudiyya, Rayyanah Barnawi da Ali Al-Qarni da wasu abokan tafiyarsu sun yi nasarar dawowa wannan duniya tamu lafiya a yau bayan shafe kwanaki 10 a tashar sararin samaniya.
Barnawi ita ce mace ta farko da ta fara makamanciyar ziyarar duniyar wata.
Rahotanni sun bayyana yadda Barnawi ta share hawayen farin cikin daga fuskantar a yayin da take shirin dawowa bayan kammala aikin da gwajin da suka je yi.
A cewarta kowanne labari yana da ƙarshensa, sai dai wannan labari nasu, labari da ya shafi buɗe sabon shafin samar da cigaba ga ƙasarta da ma yankinta.
A yayin wannan tafiya, Barnawi ta su rakiyar tsohon ma’aikacin Cibiyar Kimiyya da Fasahar Sararin Samaniya (NASA), Peggy Whitson da kuma John Shoffner.
A ranar Litinin da ta gabata ne dai, Al Qarni da Barnawi suka gudanar da gwajin musayar tsafi a sararin samaniya, inda Barnawi ta kasance mai sa-ido game da yadda wata waya ta ɗau tsafi tare da hucewa da kanta.
Wannan dai na zuwa ne cikin binciken gwamna 14 na farko a tarihi da aka yi wanda ake kallo a matsayin abin burgewa da kuma jinjina.