Home » Yau Laraba take sabuwar shekarar Musulunci na shekarar 1445 bayan Hijira

Yau Laraba take sabuwar shekarar Musulunci na shekarar 1445 bayan Hijira

by Anas Dansalma
0 comment
Yau Laraba take sabuwar shekarar Musulinci na 1445 bayan Hijira

Yau take 1 ga watan Muharram 1445 AH, biyo bayan cikar  kwana 30 ga watan Dhul Hijjah na shekarar 1444 bayan Hijirah Jiya Talata.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na III ne ya sanar da da yau Laraba, 19 ga watan Yuli a matsayin 1 ga watan Muharram na shekarar 1445 bayan Hijirah.

Jihohi da dama a ƙasar nan sun sanya yau laraba a mastaayin ranar hutu ga ma’aikata domin taya musulmin ƙasar nan murnan zagayowar shekarar kalandar musulunci ta 1445.

Jihohin sun hadar da nan Kano, da jihohin Sokoto, da Osun, zamafara, da jihar jigawa. Sai kuma jihar Kebbi da jihar Oyo, da jihar kwara.

Gwamnonin sun buƙaci al’ummar Musulmai da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’i ga jihohin da ƙasa baki ɗaya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi