Yau take babbar Sallah a ko ina a Duniya.
A jihar Kano, Mai martaba sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya gabatar da jawabin Barka da Sallah a kofar ƙwaru dake daura da masallacin juma’a na gidan Sarki.
Bayan godewa Allah s.w.a, maimartaba sarki ya yi kira da al’ummar jihar nan da su yi amfani da wannan lokutan bikin sallah wajen sada zumunta da kuma kyautata halaye a tsakaninsu da juna.
Wakilinmu Ismail Sulaiman Sani wanda ya halarci fadar da rahoton da ya haɗa mana a kai.