Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dawo ƙasar nan bayan wata ziyara da ya kai ƙasar Faransa inda ya shafe tsawon mako biyar.
A baya an bayyana cewa, dalilin tafiyar shi ne samun hutu bayan kammala yaƙin neman zaɓen da zaɓen da aka gudanar da ya tabbatar da shi a matsayin shugaban ƙasa mai jiran gado.
Tun farko an tsara cewa zaɓaɓɓen shugaban na Najeriya zai kwan biyu a Paris cikin ƙasar Faransa, daga nan kuma ya wuce zuwa birnin London, kafin ya dangana da ƙasar Saudiyya.
Sai dai rashin ganin sa a ƙasar Saudiyya lokacin aikin umrah, musamman daidai lokacin da shugaban ƙasar mai barin gado, Muhammadu Buhari yake can, ya haifar da jita-jita da raɗe-raɗi.
Tinubu ya sauka ne da yammacin a yau a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja babban birnin ƙasar nan.