A duk lokacin da jirage masu saukar ungulu suka tashi ko suka sauka a kasar nan za a fara bibiyar su dan ganin an tattarara haraji daga bangarensu.
A ganinhakan zai inganta tattara haraji a bangaren filayen jirgin sama,
Gwamnatin tarayya ta hannun ministan harkokin jiragan sama Hadi Sirika na kara duban hanyoyin da za a kara tattara haraji daga jirage masu saukar ungulu.
Hadi sirika ya ƙaddamar da rukunin wadanda suka samu horo a kan jirgi mai saukar ungulu a filin sauka da tashin jirage na kasa dake jihar Rivers.
A jawabin ministan wanda ya samu wakilci Norris Anozie, daraktan kula da harkokin ma’aikata na filayen jirgi ya bayyana matsayar gwamnati a kan habbaka HANYOYIN tattara haraji daga jirage masu saukar ungulu.
Daga karshe ya bayyana cewa Jami’ai masu lura da jiragen ne suke da alhakin tattara harajin a madadin gwamnati.