Ma’aikata daga kowane ɓangare a ƙasar nan a ciki har ma’aikatan wutar lantarki da na kiwon lafiya sun fara yajin aikin gargaɗi saboda raɗadin tsadar rayuwar da cire tallafin man fetur ya haifar.
Ma’aikatan sun yi barazanar durƙusar da al’amura a ƙasar mafi ƙarfin tattalin arziki a Afirka muddin gwamnati ta ƙi biya musu buƙatunsu.
A ganawar da suka yi a makon jiya sun yi ƙorafin cewa matakin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka na cire tallafin man fetur ya jefa ma’aikata da kuma talakawan Njeriya cikin masifa.
An yi yunƙurin fasa yajin aikin a jiya Litinin da yamma, amma abin ya ci tura, saboda shugabannin ƙungiyar ta NLC sun ƙi halartar wata ganawa da Ma’aikatar Ƙwadagon ƙasar ta so yi da su.
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadagon Joe Ajaero, ya ce cikin mako biyu za su gurgunta al’amuran yau da kullum a ƙasar, komai ya tsaya cak, idan gwamnati ba ta biya bukatun ma’aikata ba, a ciki har da ƙarin albashi.