Zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da aniyar gwmanatinsa sake fasalin kasuwannin jihar Kano tare da yin aiki ba tare da nuna bambanci ba.
Sannan ya tabbatar da cewa ‘yan kasuwa za su samu girbi a cikin gwmanatinsa musamman batun kwamishinan kasuwanci wanda zai tabbata daya ne daga cikin ‘yan kasuwa a jihar nan.
Wannan kalamai sun fito ne daga wata sanarwa da mukaddashin sakataren yada labaran gwamnan, Hisham Habib ya sanya wa hannun a yayin da yake tattaunawa da kasuwa a fadar gwamnatin jihar Kano.
Ya tabbatar da cewa gwmnatin jihar Kano za ta karfafa wa harkokin kasuwanci da a tallafa wa ‘yan kasuwa maza da mata, musamman wajen gudanar da kasuwanci na zamani.
Har’ila yau, ya bayyana shirin gwmanati na rage cunkoson da ke akwai a kasuwannin cikin birni ta hanyar samar da wasu sabbin wuraren kasuwanci domin karfafa wa ƙananan ‘yan kasuwa cin moriyar shirin.