Home » Zan Haɗa Kai da Kowa Wajen Ciyar da Katsina Gaba- Dikko Radda

Zan Haɗa Kai da Kowa Wajen Ciyar da Katsina Gaba- Dikko Radda

by Anas Dansalma
0 comment

Zababben gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda , ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki da kowanne bangare na al’umma domin tabbatar da ta ciyar da jiharsa gaba.

Radda ya ce abun da zai maida hankali akai shi ne ciyar da Katsina gaba ta hanyar kawo shirye shirye masu inganci.

Dikko Umaru Radda ya kuma ce ya yi mamaki wasu zarge-zarge da batutuwan da suka biyo bayan zaben da ya bashi nasara, sai dai kuma ba shi da wata fargaba domin ya san al’umma jihar Katsina ne suka zabe shi, saboda gamsuwa da manufofinsa.

Kan batun ‘yan adawa musamman jam’iyyar PDP da Sanata Yakubu Lado Danmarke ya yi zargin an tafka magudi da aringizon kuri’u a lokacin zaben gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Mayu, da shan alwashin daukar matakin shari’a, Dikko Radda ya ce ba ya ko dar domin ya san an yi sahihin zabe mai iganci a jihar Katsina.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi