Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa zai raya manufofin gwamnatin Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da ta shuɗe.
Majiyarmu ta rawaito cewa cikin ayyukan da Abba ya ambato zai farfaɗo da su sun haɗa da: samar da ingantaccen ilimi da shirye-shirye na ba da tallafi da koyar da sana’o’i da kammala ayyukan da aka yi watsi da su da shirin haihuwa kyauta a asibitoci da ba da jari da samar da kyakkyawan yanayin bunƙasa kasuwanci a faɗin jihar.
Abban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a yayin gabatar da jawabin godiya game da tabbatar da shi da hukumar zaɓe ta yi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwmnan jihar nan.
Sannan ya ƙara da cewa ko shakka babu gwamnatinsa za ta zama sak da irin gwamnatin Kwankwaso da ya gabace shi.
Tare da yin alƙawarin cewa gwamnatinsa ba za ta saɓa alƙawuran da ta yi ba a lokacin yaƙin neman zaɓe da ya gabata.
Sannan a ƙarshe ya godewa al’umma a bisa amincewa da shi da kuma dukkan mutanen da suka ba shi goyon baya.