Sabon shugaban jami’iyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya ce zai kama aiki ba ji ba gani domin tabbatar da jam’iyyarsa ta yi nasara a zaɓen gwamnan jihohin Kogi da Bayelsa da za a gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.
Ganduje ya bayyana haka ne a yau Alhamis, lokacin da yake jawabi bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC, a wajen taron majalisar zartarwar jam’iyyar da ya gudana a Abuja.
An kuma zaɓi tsohon mai magana da yawun Majalisar Dattijan Najeriya, Ajibola Basiru, ɗan jihar Osun a matsayin sakataren Jam’iyar.
A jawabin nasa, Ganduje ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, ya kuma jaddada cewa zai tabbatar da zaman lafiyar a cikin jam’iyar.
Ganduje ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru wajen tabbatar da nasarar jam’iyar a zaɓen gwamnan jihar Kogi da Imo da Bayelsa