• Home  
  • Ɗan Majalisar Tarayya Yaya Tongo ya rasu
- Babban Labari

Ɗan Majalisar Tarayya Yaya Tongo ya rasu

Ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye a Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo, ya rasu a ranar Juma’a a Abuja bayan doguwar jinya. Marigayi Yaya Bauchi Tongo, jigo ne a jam’iyyar APC wanda Gwamna Muhammad Inuwa ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Jihar Gombe da ma kasa baki ɗaya. Rasuwarsa ta zo ne […]

Ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye a Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo, ya rasu a ranar Juma’a a Abuja bayan doguwar jinya.

Marigayi Yaya Bauchi Tongo, jigo ne a jam’iyyar APC wanda Gwamna Muhammad Inuwa ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Jihar Gombe da ma kasa baki ɗaya.

Rasuwarsa ta zo ne kasa da maonni biyu bayan an yaɗa jita-jitar mutuwarsa  a kafafen sada zumunta, lamarin da makusantansa da magoya bayansa suka musanta a wancan lokaci.

A cikin sakon ta’aziyyar da Darakta Janar na Harkokin Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Inuwa ya bayyana marigayin a matsayin gogaggen ɗan siyasar kasa, ƙwararren ma’aikacin gwamnati kuma wakili mai kishin al’ummarsa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa jama’a hidima.

Gwamnan ya ce gudunmawar da marigayin ya bayar ba ta tsaya ga mazaɓarsa kaɗai ba, domin ya taka muhimmiyar rawa wajen ci-gaban Jihar Gombe da Najeriya ta hanyar ayyukan ci-gaban mazaɓar da kuma tallafin jin ƙai.

Sannan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar mazabar Gombe/Kwami/Funakaye, Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ‘yan Majalisar, abokan siyasarsa da daukacin al’ummar Jihar Gombe.

Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya ba shi Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansa da masoyansa hakurin jure wannan babban rashi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai