• Home  
  • Matsin Lamba Ya Fitar Da Shugaban Kasar Madagascar Andry Rajoelina
- Babban Labari - Labarai

Matsin Lamba Ya Fitar Da Shugaban Kasar Madagascar Andry Rajoelina

Rahotanni sun ce shugaban ƙasar Madagascar, Andry Rajoelina, ya fice daga ƙasar, sakamakon matsin lamba da ake yi masa na ya sauka daga mulki. Matasan ƙasar sun ɗauki kwanaki suna zanga-zangar neman ya sauka daga mulki. Kafofin yada labaran Faransa sun ce an fitar da shugaban daga ƙasar ne a cikin wani jirgin sojin Faransa […]

Rahotanni sun ce shugaban ƙasar Madagascar, Andry Rajoelina, ya fice daga ƙasar, sakamakon matsin lamba da ake yi masa na ya sauka daga mulki.

Matasan ƙasar sun ɗauki kwanaki suna zanga-zangar neman ya sauka daga mulki.

Kafofin yada labaran Faransa sun ce an fitar da shugaban daga ƙasar ne a cikin wani jirgin sojin Faransa a jiya Lahadi.

Hukumomin Faransa sun ce ba sa shisshigi a harkokin cikin gida na ƙasar .

Ƴan adawa a majalisaer dokokin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa za su fara zaman tsige Mista Rajoelina.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000