• Home  
  • Gwamnan Neja Ya Ba Iyalan Wadanda Suka Kone A Gobarar Tankar Mai N1m Kowannensu.
- Babban Labari - Labarai

Gwamnan Neja Ya Ba Iyalan Wadanda Suka Kone A Gobarar Tankar Mai N1m Kowannensu.

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan ɗaya ga duk iyalin da ya rasa ɗan uwa a gobarar tankar man da ta faru a garin Essa, Karamar Hukumar Katcha. Haka kuma, ya ba da tallafin naira dubu ɗari biyar ga kowanne daga cikin waɗanda suka jikkata a lamarin. […]

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan ɗaya ga duk iyalin da ya rasa ɗan uwa a gobarar tankar man da ta faru a garin Essa, Karamar Hukumar Katcha.

Haka kuma, ya ba da tallafin naira dubu ɗari biyar ga kowanne daga cikin waɗanda suka jikkata a lamarin.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin da abin ya shafa, inda ya tantance tare da ganawa da shugabannin al’umma da mazauna yankin.

Wannan sanarwa ta fito ne daga Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Bologi Ibrahim, a daren Alhamis.

Mummunan hatsarin gobarar tankar man ya faru ne da misalin ƙarfe 3:45 na ranar Talata, lokacin da wuta ta tashi a cikin tankar man fetur din da mutane ke diba daga tankar da ta kife a kan hanyar Bida–Badegi–Agaie.

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, Abdullahi Arah, ya tabbatar da cewa adadin waɗanda suka mutu ya kai 42, yayin da waɗanda suka jikkata suka kai 52.

Arah, wanda ya bayyana hakan a hirarsa da gidan talabijin na Arise, ya danganta faruwar lamarin da lalacewar hanya da kuma zafin rana a yankin, wanda ya taimaka wajen haifar da gobarar.

“Ina jin baƙin ciki matuƙa da faruwar wannan lamari,” in ji Gwamna Bago, yayin da yake addu’ar samun sauƙi ga waɗanda ke jinya a asibitocin Bida da Abuja.

Sai dai ya soki dabi’ar dibar man fetur daga tankar da ta kife, yana mai cewa hakan na da matukar hatsari kuma babban laifi ne.

“Mun zo ne don yin ta’aziyya da su kan asarar rayuka, da kuma tunatar da su muhimmancin kiyaye rayuka.

“Abin takaici ne a ce tankar man ta faɗi, sai mutane su fito da jarakuna suna dibar man. Wannan sata ce, kuma dole ne a dakatar da ita. Ba za mu goyi bayan hakan ba,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma ce fitaccen ɗan kasuwa, Aliko Dangote, ya yi alkawarin gyara hanyar Mokwa–Lambata, kuma aikin zai fara nan ba da jimawa ba.

A ƙarshe, gwamnatin jihar ta bayyana cewa za ta gina cibiyar kula da lafiya ta farko a garin Essa domin biyan buƙatun lafiyar al’ummar yankin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai