Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar da za su fafata a zaɓukan cike gurbi da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Yunin 2026 a wasu mazaɓu da kujerun majalisu da suka haɗa da na Majalisar Dattawa da ta Wakilai da kuma Majalisar Dokokin Jiha.
A zaɓen sanatan Ondo ta Kudu, akwai ‘yan takara hudu da suka hada da Adesanya Olaoluwa na jam’iyyar APP da Faduyile Francis Adedayo na APC da Akinwumi Adeolu Harrison na APM da kuma Nejo Funso Clement na BP.
A kuma zaɓen Sanatan Nasarawa ta Arewa, Halilu Danladi Envwulu-Aza ne zai wakilci APC, yayin da Maku Labaran ke takarar LP, John Paul Araneshri na NNPP da Emmanuel David Ombugadu na PDP.
A Jihar Rivers, kujerar Sanatan Rivers ta Kudu maso Gabas za ta kasance tsakanin Douglas Fabeeke Beeka na AA da Osarosaka Ebenezer Erewari na APC da Sam Kinanee Barikpoa na LP da kuma Nwogu Olaka Johnson na PDP.
A Enugu ta Arewa kuwa, Asogwa Ikeje Israel na APC, Aneke Kingsley Chukwuebuka na BP da Ezeme Nestor Chika na PDP ne za su fafata.
Jerin sunayen ya kuma nuna cewa a mazaɓar Zuru ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Garba Aiki Rabiu na APC da Aliyu Galadima Muhammad na LP ne za su kara da juna.
Haka kuma a mazaɓar Dawakin Kudu/Warawa ta Majalisar Wakilai a Jihar Kano, Rabiu Shuaibu na APC zai fafata da Lawan Garba Haruna na APM da kuma Abubakar Yahaya Muhammad na LP.
Ana sa ran gudanar da zabukan cike gurbin ne domin maye gurbin kujerun da suka zama babu wakilai saboda dalilai daban-daban.
INEC ta buƙaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara su bi ƙa’idojin yaƙin neman zabe tare da tabbatar da gudanar da harkokinsu cikin lumana kafin ranar kaɗa kuri’a.
