• Home  
  • Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya
- Babban Labari

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya

Jami’an tsaro sun kama mutumin da ake zargi da ƙirƙira wata hukumar ta bogi a Najeriya kuma ya naɗa kansa a matsayin Darakta Janar. An kama Adeniyi Adeyemi wanda ke ikirarin cewa shi ne shugaban hukumar ba da shawara kan haɓaka kasuwanci da ƙasashen ƙetare (PFIPC) bayan da mai shari’a Mohammed Umar na babbar kotun […]

Jami’an tsaro sun kama mutumin da ake zargi da ƙirƙira wata hukumar ta bogi a Najeriya kuma ya naɗa kansa a matsayin Darakta Janar.

An kama Adeniyi Adeyemi wanda ke ikirarin cewa shi ne shugaban hukumar ba da shawara kan haɓaka kasuwanci da ƙasashen ƙetare (PFIPC) bayan da mai shari’a Mohammed Umar na babbar kotun tarayya ya ba da umarnin kama shi.

Hukumomin ƙasar sun cafke Adeyemi ne a maboyarsa da ke jihar Osun, kuma ana sa ran za a kai shi hedkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Abuja domin ci gaba da bincike da kuma shirya gurfanar da shi a gaban kotu.

Kama Adeyemi na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan da Mai Shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin kama shi a zaman kotun na ranar Talata.

Adeyemi bai bayyana a gaban kotun ba, duk da cewa gwamnati ta ce an riga an miƙa masa sammaci.

Lauyan gwamnatin tarayya, Wisdom Madaki, ya shaida wa kotun cewa wannan ba shi ne karo na farko da wanda ake zargin ya ƙi halartar kotu ba, domin an riga an ɗage shari’ar har sau biyar saboda rashin zuwansa domin a gurfanar da shi.

Saboda haka ne ya roƙi kotun ta bayar da sammacin da zai bai wa jami’an tsaro damar kamo Adeyemi tare da gabatar da shi a gaban kotu a ranar da za a ci gaba da sauraron shari’ar.

Sai dai lauyan Adeyemi, Genesis Francis, ya ce wanda yake karewa na fuskantar barazana a rayuwarsa, kuma saboda haka ne ya kasa halartar kotun.

Lauyan ya ƙara da cewa Adeyemi ya rubuta wata buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Shugaba Bola Tinubu, inda ya nemi a ba shi kariya, domin a cewarsa batun ya zama abin tattaunawa a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa ake yi masa barazana.

Sai dai mai shari’a Mohammed Umar ya tabbatar wa lauyan cewa kotu za ta tabbatar an kare lafiyar wanda ake zargin domin ya fuskanci shari’arsa.

Daga nan ne kotun ta amince da buƙatar masu gabatar da ƙara, kuma ta bayar da umarnin kamo Adeyemi, sannan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga Satumba, lokacin da ake sa ran za a gurfanar da shi a gabatnta

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000