• Home  
  • Kenya ta hana taron jama’a saboda cutar Ebola
- Kasashen Ketare

Kenya ta hana taron jama’a saboda cutar Ebola

Ƙasar Kenya ta dakatar da gudanar da tarukan gwamnati da tarurruka a cikin otal-otal bayan ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola. Jami’an lafiya sun ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na dakile yaɗuwar cutar. A cewar hukumomi, mutumin da ya kamu da cutar, wanda ɗan […]

Ƙasar Kenya ta dakatar da gudanar da tarukan gwamnati da tarurruka a cikin otal-otal bayan ta tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Ebola.

Jami’an lafiya sun ce matakin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na dakile yaɗuwar cutar.

A cewar hukumomi, mutumin da ya kamu da cutar, wanda ɗan ƙasar Kenya ne, ya rasu a ranar Litinin bayan ya yi tafiya daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) ta cikin ƙasar Uganda kafin ya isa Kenya.

Hukumomin lafiya sun ce suna ci gaba da ɗaukar matakan kariya da sa ido domin hana yaduwar cutar zuwa wasu yankuna na ƙasar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai