• Home  
  • Adadin waɗanda suka mutu a hatsarin kwale-kwalen Bayelsa ya kai 29
- Labarai

Adadin waɗanda suka mutu a hatsarin kwale-kwalen Bayelsa ya kai 29

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwalen da ya auku ranar Juma’a a ƙaramar hukumar Southern Ijaw da ke Jihar Bayelsa ya ƙaru zuwa mutum 29, yayin da sama da mutum 50 da suka tsira ke karɓar magani a asibitoci. Gwamnan jihar, Douye Diri, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar jaje da Mataimakin […]

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwalen da ya auku ranar Juma’a a ƙaramar hukumar Southern Ijaw da ke Jihar Bayelsa ya ƙaru zuwa mutum 29, yayin da sama da mutum 50 da suka tsira ke karɓar magani a asibitoci.

Gwamnan jihar, Douye Diri, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar jaje da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai masa.

Diri ya ce har yanzu ba za a iya tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu gaba ɗaya ba, domin ana ci gaba da ƙoƙarin ciro kwale-kwalen da ya haddasa hatsarin.

Sai dai ya ce akwai yiwuwar wasu fasinjoji na nan maƙale a cikin kwale-kwalen.

Gwamnan ya yi zargin cewa kwale-kwalen bai dace da zirga-zirgar ruwa ba, sannan kuma ya tashi ne daga wata tashar fasinjoji da ba a amince da ita ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai