• Home  
  • An Yi Haniya A Zauren Majalisar Dattawa Lokacin Tantance Christoper Musa
- Babban Labari - Labarai

An Yi Haniya A Zauren Majalisar Dattawa Lokacin Tantance Christoper Musa

Majalisar Dattawan Najeriya ta shiga hayaniya yayin aikin tantance tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher  Musa a matsayin sabon ministan tsaro lokacin da wasu suka nemi ya rusuna ya wuce kawai ba tare da amsa tambayoyi masu yawa ba. Sanata Sani Musa (jihar Neja) ne ya shawarci majalisar ta bari janar ɗin ya wuce […]

Christopher Musa

Majalisar Dattawan Najeriya ta shiga hayaniya yayin aikin tantance tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher  Musa a matsayin sabon ministan tsaro lokacin da wasu suka nemi ya rusuna ya wuce kawai ba tare da amsa tambayoyi masu yawa ba.

Sanata Sani Musa (jihar Neja) ne ya shawarci majalisar ta bari janar ɗin ya wuce kawai bayan ya amsa ‘yan wasu tambayoyi marasa yawa.

Sai dai waɗanda ke adawa da hakan sun haƙiƙance cewa dole ne sai an yi masa tambayoyi masu tsauri, abin da ya jawo hatsaniya tsakanin ‘yanmajalisar.

Bayan tsawon lokaci ana hauragiya, Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya miƙe tsaye, wanda ke alamta neman kowa ya shiga taitayinsa bisa dokokin majalisar.

Da yake amsa tambayoyin, Christopher Musa ya bayyana damuwa game da ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya, kuma ya yi kira da aka kara himma wajen aiki da shirin kare makarantu na Safe School Initiative.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai