• Home  
  • Bayan Sallar La’asar Za A Yi Jana’izar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh
- Babban Labari - Labarai

Bayan Sallar La’asar Za A Yi Jana’izar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh

Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa. Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah […]

Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa.

Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya.

Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da Madina, Sheikh Abdul Rahman Sudais, sun gabatar da ta’aziyyar iyalai da ɗaliban mashahurin malamin.

Za a gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh bayan Sallar La’asar.

Kazalika za a yi masa Salatul Ga’iba a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai