Bukatunmu kan gyaran dokar zaɓen Najeriya – El-Rufai

Gyara ga dokar zabe na ci gaba da tayar da ƙura a Najeriya, inda yan’adawa suka ce tilas ne majalisar dattawan ƙasar ta amince da amfani da na’ura wajen aika sakamakon zabe nan take ta intanet.

Tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai kuma jigo a jam’iyyar hamayya ta ADC, ya ce suna son a amince da dokar zaɓen da Majalisar Wakilai ta amince.

Amincewa da gyaran dokar zaɓen da majalisar dattawan Najeriya ta yi ne ya haifar da cecekuce a Najeriya musamman kan cire sashen da ke wajabta tura sakamakon zaɓe nan take ta na’ura.

Yan’adawa da ƙungiyoyin farar huka sun soki majalisar dattawan Najeriya da ƙin amincewa da gyaran sashen da zai tilasta aika sakamakon zaɓe ta na’ura.

“Tura sakamako ta na’ura dole ne a dawo da shi, kuma dole ne a ce hukumar zaɓe ta yi aiki da shi.”

“Kuma lokacin da aka bayar na zaɓe a duba a rage shi domin ya yi yawa kuma yana wahalar da jam’iyyu da ƴantakara,” in ji Malam Nasir El-Rufai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *