• Home  
  • ICCES ta kammala shirin tabbatar da tsaro a zaɓen cike gurbin ɗan majalissar wakilan Dawakin Kudu/Warawa a Kano
- Babban Labari

ICCES ta kammala shirin tabbatar da tsaro a zaɓen cike gurbin ɗan majalissar wakilan Dawakin Kudu/Warawa a Kano

Kwamitin haɗin gwiwar jami’an tsaro kan zaɓe a jihar Kano, ICCES, ya gudanar da wani taro na musamman domin duba shirye-shiryen tsaro gabanin zaɓen cike gurbi na mazabar tarayya ta Dawakin Kudu da Warawa da za a gudanar ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026. Taron ya gudana a shelkwatar rundunar ƴan sandan jihar da […]

Kwamitin haɗin gwiwar jami’an tsaro kan zaɓe a jihar Kano, ICCES, ya gudanar da wani taro na musamman domin duba shirye-shiryen tsaro gabanin zaɓen cike gurbi na mazabar tarayya ta Dawakin Kudu da Warawa da za a gudanar ranar Asabar, 20 ga watan Yunin 2026.

Taron ya gudana a shelkwatar rundunar ƴan sandan jihar da ke Bompai, inda ya samu halartar wakilan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, da sauran hukumomin tsaro.

Da yake jawabi a wajen taron, kwamishinan hukumar zaɓe na jihar Kano, Ambasada Zango Abdu, ya ce INEC ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaɓen, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya don gudanar da sahihin zaɓe.

A nasa jawabin, kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, wanda muƙaddashin kwamishinan ƴan sanda , DCP Lawal Isa Mani, ya wakilta, ya tabbatar da cewa an kammala tsara matakan tsaro a dukkan rumfunan zaɓe, cibiyoyin tattara sakamako da sauran muhimman wurare da ke ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa.

Haka kuma, ya yi kira ga hukumomin tsaro su ci gaba da tattara bayanan sirri domin dakile duk wata barazana ga zaman lafiya, tare da gargadin jama’a da su guji yaɗa labaran ƙarya da bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

Kwamitin ya kuma jaddada cewa ba zai lamunci sayen ƙuri’u da maguɗin zaɓe ko tashin hankali ba, tare da umartar jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa, adalci da rashin nuna son kai.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar wa al’ummar mazabar Dawakin Kudu da Warawa cewa an tanadi isasshen tsaro domin gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000