Kungiyar ci gaban Haɗejia (HSDPG) ta yaba wa tsohon shugaban hukumar shigi da fici Muhammad Babandede OFR, OCM.

Ƙungiyar Hadejia Strategic Development Plan Group (HSDPG) mai ƙoƙarin samar wa ƙasar Haɗejia ci gaba mai ɗorewa, ta samu kyakkyawar tarba da liyafar cin abinci ta musamman daga hannun Shugaban Hukumar Shigi da Fici ta Nijeriya, Mai Ritaya, Muhammad Babandede, OFR, OCM, a babban birnin tarayya Abuja, gabanin fara taron tantancewa da tabbatar da Shirin Ci Gaban Yankin Arewa Maso Gabashin jihar Jigawa na Shekara 25, da aka shirya gudanarwa a yau Asabar, 17 ga Janairu.

Da yake jawabi a wajen taron, Sakataren Hukumar Tabbatar da Daidaito a Al’amura Ƙasa, Alhaji Muhammad Musa, ya nuna matuƙar godiya ga Muhammad Babandede bisa irin goyon bayan da yake bai wa ƙungiyar ta HSDPG da jikinsa da kuma aljihunsa, yana mai bayyana gudummawar tasa a matsayin ginshiƙin samun nasarar shirin.

Shi ma Farfesa Usman Haruna ya gode masa bisa haɗin kai da cikakken goyon bayan da yake bai wa shirin, yana mai tabbatar da cewa za a fitar da sakamakon da aka cim ma a shirin ga jama’a domin su san halin da ake ciki, da kuma tafiya tare.

A nasa jawabin, Muhammad Babandede, OFR, OCM, ya yaba da jajircewar mambobin ƙungiyar ta HSDPG a wannan aiki mai tarihi da zai sauya fasalin ci gaban yankin.

Ya kuma shawarci Sakatariyar ƙungiyar da ta rubuta tare da adana dukkan matakan da aka bi wajen tsara shirin na shekaru 25, yana mai cewa hakan zai iya zama abin koyi ga sauran jihohi a fadin Najeriya. Daga ƙarshe ya yi musu fatan alheri da samun nasarar shirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *