• Home  
  • Kwastam ta ƙwace kayayyakin miliyan N98.3 a Adamawa da Taraba
- Babban Labari

Kwastam ta ƙwace kayayyakin miliyan N98.3 a Adamawa da Taraba

Hukumar Kwastam reshen jihohin Adamawa da Taraba ta yi nasarar cafke lita 32,860 na man fetur da aka loda a cikin jarkoki guda 1,288 masu ɗaukar lita 25, da kuma lita 2,800 na man dizal a cikin jarkoki 112, waɗanda kuɗinsu ya kai Naira N98,375,325. Shugaban Hukumar na shiyyar, Mohammed Tanko ne ya bayyana hakan […]

Hukumar Kwastam reshen jihohin Adamawa da Taraba ta yi nasarar cafke lita 32,860 na man fetur da aka loda a cikin jarkoki guda 1,288 masu ɗaukar lita 25, da kuma lita 2,800 na man dizal a cikin jarkoki 112, waɗanda kuɗinsu ya kai Naira N98,375,325.

Shugaban Hukumar na shiyyar, Mohammed Tanko ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana a Yola ranar Laraba. Ya jaddada cewa, nasarorin da aka samu sun biyo bayan bayanan sirri ne da jami’an hukumar suka yi amfani da su a wurare daban-daban na shiyyar.

Tanko ya bayyana cewa, a cikin watanni shida da suka gabata, hukumar ta kama kayayyaki da suka haɗa da man fetur da dizal, gwanjon tufafi, ɗanyen fatar jakuna, da busashen naman jakuna, tare da magungunan da ba su da rajista, waɗanda aka yi niyyar fita da su ƙasar waje ta kan iyakokin Kamaru.

Ya ce, an yi waɗannan kamun ne a yankin Likitaba-Gembu da ke jihar Taraba, da kuma hanyar Maiha-Bellel da iyakar Sahuda a Mubi na jihar Adamawa.

“A dunƙule, an ƙwace jarkoki 1,288 da durom 3 ɗauke da kimanin lita 32,860 na man fetur, tare da lita 2,800 na dizal a cikin jarkoki 112, da sauran kayayyakin da aka lissafa. Jimillar kuɗin harajin kayayyakin ya kai N98,375,325.00 (Naira miliyan casa’in da takwas da dubu ɗari uku da saba’in da biyar da ɗari uku da ashirin da biyar).

“Wannan cikakken bayani ne kan nasarorin da muka samu na ƙwace man fetur, dizal, gwanjon tufafi, ɗanyen fatar jakuna, da busashen naman jakuna, gami da magungunan da ba su da rajista da hukumar ta samu a cikin makonni shida (6) yayin gudanar da ayyukanmu na daƙile fasa-kwauri da kare tattalin arzikin Najeriya.

“Yayin gudanar da ayyuka daban-daban bisa bayanan sirri a wurare da lokuta daban-daban a cikin yankinmu, jami’an hukumar sun samu nasarar yin waɗannan kamun.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai