Ƙungiyar Likitoci Masu Neman kwarewa n
a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Rasheed Shekoni (RSFUTH), Dutse, ta sanar da shigarta gaba ɗaya cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya da Ƙungiyar Likitocin Koyon Aiki ta Ƙasa (NARD) ta ayyana, wanda zai fara daga safiyar Litinin, 12 ga Janairu, 2026.
Sanarwar ta fito ne cikin wata takarda da Ƙungiyar Likitocin Koyon Aiki ta RSFUTH Dutse (ARD-RSFUTH) ta fitar a ranar Alhamis, wadda Mukaddashin Shugaban ƙungiyar, Dakta Aminu Yahaya, da Mukaddashin Sakatare, Dakta Shamsu Sa’idu, suka sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, yajin aikin zai kasance cikakke, gaba ɗaya kuma na dindindin, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12:00 na dare (tsakar dare) a ranar Litinin, bisa umarnin Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) ta NARD.
Sanarwar ta ce, “Dukkan likitocin koyon aiki a RSFUTH Dutse za su janye ayyukansu gaba ɗaya kuma ba tare da wa’adin komawa ba daga ranar da yajin aikin ya fara.”
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa za ta shirya zanga-zangar lumana a ranar Litinin ɗin, domin nuna goyon baya ga yajin aikin na ƙasa da kuma matsa lamba kan gwamnati ta biya buƙatun ƙungiyar.
ARD-RSFUTH Dutse ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki ya zama dole sakamakon gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika yarjejeniyar fahimta (MoU) da aka cimma da NARD, duk da dogon tattaunawa, shawarwari masu ɗorewa da kuma alkawurran da aka sha bayarwa.
Daga cikin muhimman buƙatun NARD akwai dawo da likitocin koyon aiki da aka kora a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Lokoja, biyan dukkan basussukan albashi, karin girma da alawus-alawus da ake bin likitocin koyon aiki a faɗin ƙasa, da kuma aiwatar da jadawalin alawus na ƙwararru (PAT) yadda ya kamata, ciki har da bashin da ya taru.
Sauran buƙatun sun haɗa da biyan alawus na ƙwarewa (Specialist Allowance) ga duk likitocin da suka cancanta, warware matsalar jinkiri da bashin albashin likitocin koyon aiki na matakin farko (House Officers), fitar da cikakkiyar sanarwar biyan albashi daga Hukumar Kula da Likitoci da Likitocin Haƙori ta Ƙasa (MDCN), da samar da tsari guda ɗaya kan tsallake mataki da matakin fara aiki a dukkan cibiyoyi.
Ƙungiyar ta kuma nemi a warware dukkan matsalolin biyan kuɗi da suka samo asali daga ƙarin albashi na kashi 25 da 35 na CONMESS da alawus na kayan aiki ta hanyar IPPIS, da kuma ci gaba tare da kammala tattaunawar Yarjejeniyar Ciniki ta Ƙungiyoyi (CBA).
Haka kuma, likitocin sun buƙaci ɗaukar matakin gaggawa domin gyara lalacewar gine-ginen asibitoci da kuma tsofaffin kayan aikin likitanci da ke barazana ga ingancin ayyukan lafiya.
Duk da bayyana damuwa kan wahalhalun da yajin aikin zai haifar wa marasa lafiya da al’umma, ARD-RSFUTH Dutse ta ce sakaci da jin daɗin likitoci da durƙushewar tsarin lafiya ya bar musu babu wata mafita face ɗaukar wannan mataki.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa ana iya kauce wa yajin aikin da zanga-zangar lumana idan har gwamnati ta nuna cikakkiyar niyya ta hanyar ɗaukar matakai masu gamsarwa, na lokaci da kuma a bayyane wajen biyan waɗannan buƙatu.
