Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce nanata cewa kasarsa ta mika wuya ga batun zaman lafiya da Donald Trump, ke yi ba daidai ba ne.
Mr Zelensky, ya shaida wa wata kafar yada labarai cewa yana fatan dai duk dabara ce hakan da Trump din ke yi.
A baya bayannan sau biyu shugaban na Amurka na cewa ya ragewa Ukraine ta tabbatar da an samu nasara a tattaunawar zaman lafiyar da ake a Geneva ba tare da ambaton Rasha ba.

