Daraktan cibiyar yaƙi da ta’addanci na ƙasar Amurka ya sanar da ajiye aiki a shafinsa na soshiyal midiya, inda ya ce “tunaninsa bai amince masa ya goyi bayan yaƙin da ake yi kan Iran ba”.
Majalisar dattawan Amurka dai ta tabbatar da Joe Kent a matsayin mutumin da Trump ya zaɓo domin cike gurbin a watan Yulin bara.
Da yake yi wa Trump bayani a wasiƙar ajiye aikin, Kent ya ce “Iran ba ta barazana ga ƙasarmu, kuma a bayyane take cewa mu ne muka fara wannan yaƙi saboda matsin lamba daga Isra’ila da masu neman mata gindin zama masu ƙarfin faɗa a ji.
“Ina goyon bayan akidu da tsare-tsaren ƙasashen waje da ka yi kamfe da su a 2016 da 2020 da 2024 waɗanda kuma ka ɗabbaƙa a zangon mulkinka na farko.
“Har zuwa watan Yunin 2025, ka fahimci cewa yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya tarko ne aka ɗanawa Amurka na ƙarar da rayukan Amerikawa da arziƙi da cigaban dorewar ƙasarmu.
“A matsayina tsohon soja wanda ya je yaƙe-yaƙe har sau 11 kuma mutumin da ya rasa matarsa a yaƙin da Isra’ila da ƙirƙira, babu yadda za a yi na goyi bayan aikewa da matasa domin yin faɗa da ba zai amfani Amurka ba..”
Kawo yanzu dai za a iya cewa Kent ne mutum na farko da ya ajiye aikinsa bisa rashin amincewa da yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran.

