Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Ta Haramta Auren Jinsi
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta ayyana dokar haramta auren jinsi da luwadi da madigo da sauran dabi’u masu kama da su a kasar. Kazalika gwamnatin ta kuma ayyana addinin Musulunci a matsayin addini na kasa. Gwamnatin ta dauki wannan matakai ne a sabuwa dokar tsarin mulkin rikon kwarya ta kasa da babban taron muhawara na […]