Sarkin Kano Na 15 Ya Haƙura Da Hawan Sallah
Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana janye gudanar da Hawan Sallah Ƙarama na wannan shekarar, yana mai bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda dalilin tsaro da halin da Kano ke ciki a halin yanzu.