Harin Lassa: Zulum ya tura tawaga ta musamman yankin, an rufe wasu makarantu
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya tura tawaga ta musamman zuwa garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira/Uba bayan harin da ’yan ta’adda suka kai makarantar sakandaren gwamnati ta Lassa. Tawagar ta samu jagorancin Kwamishinan Ilimi, Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙire-Ƙirƙire, Injiniya Lawan Abba Wakilbe. Haka kuma ta haɗa da Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi, Samaila […]