Tinubu Na Neman Majalisa Ta Amince Masa Ya Ciyo Sabon Bashin Tiriliyan 1.150
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon shirinsa na ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 1.150, don cike gibin kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2025. Buƙatar na kunshe ne cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata. A cikin wasiƙar, Shugaba Tinubu ya […]