Gwamnatin Jigawa za ta haɗa gwiwa da Masar kan noman dabino da dankali
Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara tattaunawa da wani kamfanin bincike da raya tsirrai na Masar, EFC Plants, domin samar da haɗin gwiwa kan amfani da fasahar zamani ta tissue culture wajen noman dabino da dankalin Turawa (Irish) a jihar. Gwamnan na Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya jagoranci wata tawagar ƙwararru da masu zuba jari […]