An Kama ‘Yan kasashen Waje 193 Saboda Damfara A Legas
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta kai wani samame mafi girma na yini guda a tarihin kafuwar ta kan wasu da ake zargin masu damfara ne ta kafar intanet, inda ta cafke wasu ‘yan kasashen waje 193 da wasu ‘yan Najeriya 599 a Legas.