Mutane 5 sun mutu sakamakon rushewar gine-gine a Kano
Aƙalla mutane biyar ne suka mutu, yayin da aka ceto wasu tara bayan rushewar wasu gine-gine biyu a sassa daban-daban na Jihar Kano a ranar Asabar, sakamakon ruwan sama mai ƙarfi. Ginin farko ya rushe ne a yankin Gaida Sabon Titi, a kan hanyar gidan man Salbas da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, inda wani bene […]