Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu
Allah Ya yi wa Mai martaba Sarkin Gumel, Alhaji Dakta Ahmed Muhammad Sani II, CON, rasuwa. Rasuwar Sarkin ta jefa al’ummar Masarautar Gumel da sauran al’ummar Jihar Jigawa cikin jimami da alhini, musamman kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan sarakunan gargajiya da suka daɗe suna taka muhimmiyar rawa wajen jagoranci da zaman lafiyar al’umma. Sarkin ya […]