Abin Da Dokar Haramta “Kauyawa Day” A Kano Ta Kunsa
Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da Bikin “Kauyawa Day” a fadin jihar, tare da fitar da matakai guda shida da za su tabbatar da bin wannan doka da kuma cikar manufofin da aka sanya a gaba.