Masu Haƙar Kabari Sun Koka Kan Rashin Samun Alawus A Kano
Masu haƙa kaburbura da gyara maƙabarta sun koka kan ƙarancin alawus ɗin da ake ba su na naira 3000 a wata. Wani mai haƙar kabari a maƙabartar unguwar Tudun Wada da ke Kano, Malam Suleiman Mohammed ya shaida wa majiyarmu cewa a wasu lokutan akan biya su ƙasa da naira dubu uku, yayin da mafi […]