An gano wurin da ’yan Boko Haram suke ɓoye man fetur a ƙarƙashin ƙasa
Rundunar Operation Haɗin Kai ta Sojin Nijeriya ta sanar da gano wani wuri da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ke ɓoye man fetur, magunguna da sauran kayayyakin aikinsu a ƙarƙashin ƙasa. Samun wannan nasarar na zuwa ne bayan jerin samamen da dakarun rundunar Operation Desert Sanity suka kai a yankunan Timbuktu Triangle da ke Jihar Borno. […]