An Gurfanar Da Shamsiyya Da Tawagar Ta
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, ta bayyana cewa ta gurfanar da Shamsiya Adamu a gaban kotu bayan sake kama karin mutane 4 da kwato wayoyin sata 12 da ake zargin suna cikin gungun mutanen da ta ke jagoranta wurin sata da damfarar jama’a.