Sarkin Musulmi Ya Roƙi ‘Yan Najeriya Su Cigaba Da Yiwa Shugabanni Addu’a.
Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammadu Sa‘ad Abubakar na uku ya yi kira ga al’ummar Najeriya su cigaba da saka shugabanni cikin addu’oinsu na yau da kullum. Sultan ya yi wannan kiran ne a jami’ar Illorin a jiya Alhamis a yayin gabatar da lakcar ƙaddamar da wani littafi domin girmamawa ga farfesa Ishaq Oloyede. […]