Gwamna Namadi Ya Jaddada Aniyar Sa Ta Daƙile Cutar Tamowa a Jihar Jigawa
Gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi ya ƙaddamar da wani kwamati daga cikin majalisar zartarwar Jihar wanda zai kula da harkokin abinci mai gina jiki da ake wa laƙabi da “nutrition 774”.
Namadi ya Jaddada aniyar sa ta daƙile matsalar tamowa da kuma inganta samar da abinci a fadin Jihar.