CP Bakori ya gana da masu ruwa da tsaki kan tsaro a Tudunwada.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya kai ziyarar duba halin tsaro da ganawa da al’umma a yankin Tudun Wada domin karfafa hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da jama’a. Ya ce ziyarar ta bashi damar samun bayanai kai tsaye kan halin tsaro a kananan hukumomin, Tudun Wada da Doguwa da Sumaila da Kiru, […]