Ma’aikatan VOA Sun Maka Shugaba Trump A Kotu
Wasu daga cikin ma’aikatan kafar yaɗa labaran Muryar Amurka (VOA), sun maka shugaba Donald Trump, a gaban Kotu bisa zargin sa da rufe kafar yaɗa labaran ba bisa ƙa’ida ba.
Wasu daga cikin ma’aikatan kafar yaɗa labaran Muryar Amurka (VOA), sun maka shugaba Donald Trump, a gaban Kotu bisa zargin sa da rufe kafar yaɗa labaran ba bisa ƙa’ida ba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA.