Gobarar Daji Da Iska Mai Ƙarfi Sun Afkawa Isra’ila
Wata gobara mai karfin gaske da iska sun afkawa dazukan kasar Isra’ila, inda aka ce al’amarin na cigaba da tsananta daga daren jiya Laraba zuwa wayewar yau Alhamis, abin da ya tilastawa Firaminista Benjamin Netanyahu sanar da dokar ta ɓaci tare da neman agajin ƙasashen duniya don murƙushe wutar wadda ta durfafi dazukan da ke gab da shiga birnin Ƙudus.