An Sace Mai Anguwa Da Wasu Mutane 11 A Kaduna
‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace Mai Anguwan Babangida a masarautar Kauru, Malam Babangida Sogiji da wasu mutane 11 a wasu tagwayen hare-hare da aka kai a kauyukan Libere da Unguwan Babangida a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.