Tinubu za mu zaba a 2027 —Sheikh Jingir

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne zabinsu a babban zabe na 2027.

Sheikh Jingir, wanda shi ne Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ya bayyana zabin Tinubu ne a yayin taron kara wa juna sani na shekarar 2026 da kungiyar ta shirya a garin Jos.

Ya ce kungiyar ta yanke shawarar goyon bayan Tinubu idan bai ci amanar ’yan Najeriya ba. A cewarsa, sun riga sun yi masa alkawarin goyon baya domin ya yi wa’adi na biyu, kuma ba za su saba alkawarin ba.

“Mu ba masu karya alkawari ba ne. A zaben da ya gabata mun zabe Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu. Mun zabe ka ne domin ka inganta rayuwar mutanen Najeriya.

“Kada ka ba mu kunya, idan ka yi kuma, mu Allah Ne karfinmu. Za mu goya maka baya ka sake tsayawa takara. Mun yi alkawarin sake zaben ka tare da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a 2027,” in ji shehin malamin.

Ya bayyana imanin cewa Tinubu ba zai ci amana ba, kuma shi da mataimakinsa suna da kyakkyawar alaka, sabanin jita-jitar zaman doya da manja tsakaninsu da ake yadawa.

“Kun taba jin inda Shugaba Tinubu ya zagi Shettima ko ya ci mutuncinsa? Shugaban Kasa yana kaunar mataimakinsa. Kun taba ji ko sau daya Shettima ya soki Shugbaba Tinubu? Masu son ganin su a rana kun ji kunya, saboda ba mu taba ganin suna fada ba, kuma za su gama wa’adinsu na biyu lafiya.

“Mun yi imani cewa Tinubu na kaunar Shettima, kuma da Karfin Ikon Allah za su sake cin zabe. Zan sake zaben su, amma bisa sharadin idan sun cika alkawari.” a cewa Sheikh Jingir.

Ya shawarci Tinubu da ya yi adalci ga kowane dan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, yana mai jaddada cewa Musulunci ba addini ne da aka gina shi bisa turbar kabilanci ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *