Tsohon shugaban hukumar shigi da fici Muhammad Babandede OFR, OCM, ya buƙaci ma’aurata su dinga haƙuri da juna.

Tsohon shugaban Hukumar shigi da fici ta Najeriya Muhammad Baban Dede OFR, OCM, ya yi kira ga ma’aurata su dunga haƙuri da junansu a yanayin zamantakewa tare domin rage mutuwar
aure da ake yawan samu a wannan lokaci.Muhammad Baban Dede, ya yi wannan kiran ne, Jim kadan bayan kammala ɗaurin auren, Ibrahim Abdullahi Faskari da Amaryarsa Aisha Muhammad Idris, wanda aka gudanar a masallacin Juma’a na Zhera dake unguwar zoo road a jihar Kano a ranar asabar din nan.

Muhammad Babandede, OFR, OCM

Da yake jan hankalin ma’auratan tsohon shugaban hukumar shigi da fici , ya bayyana cewa hakuri ne ginshiƙin zamantakewar rayuwa kuma shi ne, mafi dacewa ga ma’aurata musamman a wannan zamanin na tsadar rayuwa.

Magajin Rafin Hadejia, Alhaji Muhammad Babandede

Anasa bangaren magajin Rafin Hadejia, Muhammad Babandede, ya bukaci ango da amaryar da su zauna lafiya.

Ango da amaryarsa, Ibrahim Abdullahi Faskari da Aisha Muhammad Idris, sun bayyana farin cikinsu tare da yin godiya ga yan uwa da abokan arziki , tare da godewa iyayensu musamman wadanda suka jajircewa wajen tabbatar da aurensu.

Ga rahotan Usaina Isma’il Rano

Ango Ibrahim Abdullahi Faskari

Amarya Aisha Muhammad Idris

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *