• Home  
  • UBEC ta ƙaddamar da shirin bunƙasa ilimi na Dalar Amurka 552 a Nijeriya
- Babban Labari

UBEC ta ƙaddamar da shirin bunƙasa ilimi na Dalar Amurka 552 a Nijeriya

Hukumar kula da ilimi matakin farko ta ƙasa (UBEC) ta ƙaddamar da wani babban shiri na inganta ilimi da ya kai darajar dala miliyan $552, domin tallafa wa sama da yara miliyan 29 a faɗin Najeriya. Shirin wanda aka yi wa lakabi da HOPE-EDU da HOPE-Governance, na samun goyon bayan Bankin Duniya (World Bank) da […]

Hukumar kula da ilimi matakin farko ta ƙasa (UBEC) ta ƙaddamar da wani babban shiri na inganta ilimi da ya kai darajar dala miliyan $552, domin tallafa wa sama da yara miliyan 29 a faɗin Najeriya.
Shirin wanda aka yi wa lakabi da HOPE-EDU da HOPE-Governance, na samun goyon bayan Bankin Duniya (World Bank) da kuma Global Partnership for Education, kuma ya yi daidai da manufofin gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na bunƙasa fannin ilimi.
A cewar UBEC, shirin zai haɗa da gina sabbin ajujuwa guda 13,000, horar da malamai kusan 500,000, da kuma dawo da yara da dama da ba sa makaranta zuwa tsarin karatu.
Hukumar ta jaddada cewa nasarar wannan shiri za ta dogara ne da yadda gwamnatocin jihohi za su aiwatar da shi yadda ya kamata, tare da tabbatar da gaskiya, haɗin kai, da kuma kulawa ta musamman ga ‘yan mata da yara masu buƙata ta musamman.
A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyarta na haɗa wannan shiri cikin tsare-tsaren gyaran ilimi na jihar, domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga kowa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai