• Home  
  • Yadda muka yi ƙoƙarin sasanta Iran da Amurka a gasar Kofin Duniya – Infantino
- Wasanni

Yadda muka yi ƙoƙarin sasanta Iran da Amurka a gasar Kofin Duniya – Infantino

Shugaban Hukumar kwallon ƙafa ta Duniya Gianni Infantino ya musanta wasu manya-manyan ruɗani da aka samu lokacin wasan tare da yaba wa Iran kan halartar gasar duk da rikicin da ke tsakaninta da ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi Amurka. A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Istagram wanda Fifa ta ƙara turawa […]

Shugaban Hukumar kwallon ƙafa ta Duniya Gianni Infantino ya musanta wasu manya-manyan ruɗani da aka samu lokacin wasan tare da yaba wa Iran kan halartar gasar duk da rikicin da ke tsakaninta da ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi Amurka.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Istagram wanda Fifa ta ƙara turawa mutum miliyan takwas da ke binta – Infantino ya yi bayani ga wadanda suka laɓe suna ta rubutu a bayan fage suna sukar su, maimakon yin abin da ya kamata.

Infantino ya shawarci masu suka da su mayar da hankalinsu kan kwallon kafa su ji daɗin wasannin da ake yi ba su riƙa yaɗa jita-jita ba kan shugabancinsa da Fifa game da Gasar Kofin Duniya.

Ya ce gasar Kofin Duniya ta “nuna mutuntaka da matuƙar matsayi” yana cewa gasar 2026 “ta samar da tsaro da kwanciyar hankali, farin ciki da murna ga masu bibiyarta”.

Ya ce Fifa “ta yi ƙoƙari ba dare ba rana ta haɗa kan ƙasashe biyu da ke yaƙi da juna”, kuma Iran ta shiga ƙasar wasa ” ba tare da wani rikici ba”.

Bayanan sa sun ci karo da na kocin Iran Amir Ghalenoei, wanda ya ce “tawagarsa ce wadda ta fi shan wuya” a gasar Kofin Duniya.

An hana Iran biza a kan lokaci an kuma hana wasu jagororin da suke horar da tawagar biza baki ɗaya, wasu magoya bayan da suka sayi tikitinsu duka an ƙwace, kuma an tilsata wa Iran barin inda aka tanadar mata domin atisaye a Tucson a Arizona zuwa Tijuna da ke Mexico.

Daga baya kuma suka fuskanci tsaiko na hana tafiya tsakanin wurin atisayensu da kuma inda suke wasa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000