Kungiyar kiristocin ta Ƙasa, CAN, reshen Arewacin kasar nan ta bukaci duk mabiyanta da su kwantar da hankalinsu biyo bayan ayyana Bola Ahamad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar nan da Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta yi.
Reshen kungiyar ta Arewa ta ce akwai mabiyan su da ba su ji daɗin sakamakon zaben ba, Inda suka yi zargin ba a yi musu adalci ba, amma ƙungiyar ta jan hankalinsu kan cewa ba a samun nasara ta hanyar fito-na-fito.
Shugaban matasan Pastor Musa Misal ya ce; duk da cewa da yawa ba su goyi bayan APC a kan tsai da dan takarar shugabancin kasa musulmi kuma mataimakinsa musulmi ba, yin zanga-zanga ko furta kalamai marasa dai ba su ne hanyar samun maslaha ko maganin lamarin ba. Ya kara da cewa, idan akwai matakin da ya dace a dauka ga wadanda ba su gamsu ba to kamata ya yi su tafi kotu.
Shugaban matasan ya kara da cewa, kungiyarsu ta hada hannu da mutane daga sassan Arewacin ƙasar nan daban-daban a lokacin zaben don kawo zaman lafiya a ya yin gudanar da zaben, amma abin mamaki shi ne akwai wasu wurare da ba a yi zaɓe ba a jihar Neja, sai dai kuma an samu sakamakon zabe.